M.Sh 31:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.”
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.