M.Sh 31:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.