M.Sh 29:25 - Sabon Rai Don Kowa 202025 Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki25 Sa'an nan jama'a za su ce, ‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa'ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.