Masu zunubi a Sihiyona sun firgita; rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa, “Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci? Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”
Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku.