13 Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.
13 “Kada ku riƙe ma'aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami.
Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya,
Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.
Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.
Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.