M.Sh 2:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Dukan shekarun da muka yi a tafiyarmu daga Kadesh Barneya zuwa lokacin da muka ƙetare Kwarin Zered, sun kai shekaru talatin da takwas. A lokacin, wannan tsara gaba ɗaya ta mutanen da suka isa yaƙi sun mutu daga sansani, yadda Ubangiji ya rantse musu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.