16 In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,
16 Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani,
Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina, gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina, suna numfasa tashin hankali.
Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.
Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.
Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.