Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 18:12 - Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

12 Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al'ummai a gabanku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 18:12
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.


Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku.


gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.


Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.


Kada dai ku manta da Lawiyawan da suke zama a biranenku, gama ba su da rabo, ko gādo na kansu.


na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe,


Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.


Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.


Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ