Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar?
“ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.
Sai wani mutum ya ce wa Shawulu, “Duba, ga mutane suna zunubi ga Ubangiji, suna cin nama da jini.” Shawulu ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse zuwa wurina nan da nan.”
Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.