Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.
Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila.