manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace.
Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can.
A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.