A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.
“Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.
Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.”
“Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.
Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
Za su sāke gina kufai na dā su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa; za su sabunta biranen da aka rurrushe da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.