Mika 6:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Da me zan zo gaban Ubangiji, In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama? Ko in zo gabansa da maraƙi bana ɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
“ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga.