Mika 6:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?