Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu.
“Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji. “Na zama wa Isra’ila hamada ne ko ƙasa mai babban duhu? Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo; ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”
Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.