Mika 2:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Kun kori matan mutanena daga gidajensu masu daɗi. Kuka kawar da albarkata har abada daga wurin ’ya’yansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Kukan kori matan mutanena Daga gidajensu masu kyau, Kukan kawar da darajata har abada daga wurin 'ya'yansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’