Mika 1:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.