Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 4:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

6 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa, ‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’ da kuma ‘Za su tallafe ka, Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 4:6
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?


Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.


Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne.


yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.


Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’”


Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.


Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ