Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
“Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa.
“ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’
“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),