Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 24:10 - Sabon Rai Don Kowa 2020

10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

10 A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 24:10
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.


“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.


Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”


Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.


A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.


Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.


“Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.


gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.


Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes.


Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”


annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ