Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 23:23 - Sabon Rai Don Kowa 2020

23 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

23 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 23:23
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.


Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.


Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.


Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”


Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.


Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.


“ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.


Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’


Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’ da ba ku zargi marar laifi ba.


Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba?


Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.


“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ