Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.”