Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”
Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.