Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka.
Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.
Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.