Markus 6:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”