1 Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.
1 Ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi.
ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”
Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su.
Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”