Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.