“Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.
Gama na sani yadda kuke ’yan tawaye da masu taurinkai. In kuna yin tawaye ga Ubangiji tun ina da rai tare da ku, yaya tawayen da za ku yi masa bayan na rasu!
Idan mutum ya auri mata, daga baya ba tă gamshe shi ba domin ya gano wani abu marar kyau game da ita, ya ba ta takardar saki, ya kuma kore ta daga gidansa,