Malaki 2:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.