Malaki 2:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;