Makoki 2:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”