Mahukunta 9:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni, ’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.