Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 9:28 - Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

28 Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 9:28
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.


Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.


Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.


Da dukan Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, “Ina ruwanmu da Dawuda! Ai! Ba mu da gādo wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ila, kowa yă koma tentinsa! Dawuda, sai ka lura da gidanka!” Saboda haka Isra’ilawa suka watse zuwa gida.


Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”


To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi.


Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.


Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da ’yan’uwansa daga Shekem.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ