13 Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres.
13 Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres.
Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu.
Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin.