Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 21:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Suka ce, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, “Me ya sa wannan abu ya faru da Isra’ila? Don me kabila ɗaya daga Isra’ila za tă ɓace a yau?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

3 Suka ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa wannan abu ya faru a cikin Isra'ila, har da za a rasa kabila guda ta Isra'ila?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 21:3
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?


Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka.


Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.


Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?


Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?


Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?”


Sai mutanen suka tafi Betel, inda suka zauna a gaban Allah har yamma, suna tā da muryoyinsu suna kuka mai zafi.


Kashegari da sassafe mutane suka gina bagade suka miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ