Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 21:10 - Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

10 Taron jama'a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 21:10
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.


Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi.


Mala’ikan Ubangiji ya ce, ‘Ka la’anci Meroz.’ ‘Ka la’anci mutanensa sosai, domin ba su kawo wa Ubangiji taimako ba, su kawo wa Ubangiji taimako a kan masu ƙarfi ba.’


Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ”


Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor.


dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa.


Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji,


Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron.


Gama da aka yi ƙidaya mutane, sai aka gane cewa babu wani daga mutanen Yabesh Gileyad da yake a can.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ