Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 19:9 - Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

9 Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka dādi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 19:9
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.


Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.


Saboda haka suka zauna su biyu suka ci suka sha tare. Bayan haka sai mahaifin yarinyar ya ce, “Don Allah ka kwana ka ji wa kanka daɗi.”


Da sassafen kashegari rana ta biyar, ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ka ɗan zauna ka shaƙata sai rana ta yi sanyi mana!” Saboda haka su biyu suka zauna suka ci abinci tare.


Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa.


Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta.


Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ