Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 13:8 - Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Sai Manowa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, bari mutumin Allahn da ka aiko mana yă sāke zuwa don yă koya mana yadda za mu goyi yaron da za a haifa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

8 Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 13:8
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”


Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’


Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa.


Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba.


Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”


Allah ya ji Manowa, sai mala’ikan Allah ya sāke zuwa wurin matar yayinda take gona; amma Manowa mijinta ba ya tare da ita.


Manowa ya tashi ya bi matarsa. Da ya zo wurin mutumin, sai ya ce, “Kai ne wanda ka yi magana da matata?” Ya ce, “Ni ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ