Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 9:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

16 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 9:16
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.


Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.


Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.


Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.


Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.


Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.


Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.


Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”


bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”


In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?


Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa,“Effata!” (Wato, “Buɗe!”).


Da zarar kun shiga garin, za ku same shi kafin yă tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu. Gama jama’a ba za su ci ba, sai ya kai can ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura da sauri, za ku same.”


Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna.


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ