Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 6:35 - Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

35 Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 6:35
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”


Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.


Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.


Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.


Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.


Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.


Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.


Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.


Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”


Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,


Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”


Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”


Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.


Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.


Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ