Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”
A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.