Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.
Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.
Yoshuwa ya ce wa dukan mutanen, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Dā can, kakanninku, Tera mahaifin Ibrahim, da Nahor sun zauna a hayin Kogin Yuferites suka yi wa waɗansu alloli sujada.