Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa.
“Gama zan ba da umarni, zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila a cikin dukan ƙasashe kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.
Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.