Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 21:36 - Sabon Rai Don Kowa 2020

36 Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

36 Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 21:36
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.


Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.


“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.


“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.


Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.


Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.


Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa.


Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.


To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.


Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”


Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.


Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”


Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.


Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.


Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.


Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.


Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?


amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.


Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ”


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”


Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.


Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.


Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi.


Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.


Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.


Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”


Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu.


Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.


Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ