Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya,
Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka.
“ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura.