An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,
“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.
Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.
amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.
domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.
Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar