Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.
Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”
“Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.