Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.
Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.
Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.
Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi, wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace? Wane ne ya koya masa sani ko ya nuna masa hanyar fahimta?