Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.
“Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ”
“Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi.
A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.