Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 7:89 - Sabon Rai Don Kowa 2020

89 Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

89 Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 7:89
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.


Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza.


Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka


Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.


A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma.


Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.


Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”


Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,


Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,


Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.


Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.


Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ